Skip to content
Ayyukan Manzanni 10:3-6

Ayyukan Manzanni 10:3-6

3
Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”
4
Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
5
Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.
6
Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options