2 Sama’ila 22:4-7
4
“Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.
5
Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
6
Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini.
7
“A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.
Settings