Skip to content
2 Sama’ila 22:30-37

2 Sama’ila 22:30-37

30
Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
31
“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
32
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
33
Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
34
Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
35
Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
36
Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
37
Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options