2 Sama’ila 18:31-33
31
Sai ga mutumin Kush ya iso ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, ka ji labari mai kyau! Ubangiji ya cece ka yau daga dukan waɗanda suka tayar maka.”
32
Sarki ya ce wa mutumin Kush, “Saurayin nan Absalom, yana nan lafiya?” Mutumin Kush ya ce, “Allah yă sa abokan gāban ranka yă daɗe, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”
33
Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”
Settings