Skip to content
2 Sama’ila 18:1-5

2 Sama’ila 18:1-5

1
Dawuda ya tattara mutanen da suke tare da shi, ya naɗa musu komandodi na dubu-dubu, da na ɗari-ɗari.
2
Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”
3
Amma mutanen suka ce, “Ba za ka fita ba; gama in ya kasance tilas mu gudu, ba za su kula da mu ba. Ko da rabinmu sun mutu, ba za su damu ba; amma kai kanka ka fi mutum dubu goma namu. Zai fi maka ka zauna a cikin gari, ka dinga aika mana da taimako.”
4
Sarki ya ce, “Zan yi duk abin da ya fi muku kyau.” Saboda haka sarki ya tsaya kusa da bakin ƙofa yayinda dukan mutane suke fitowa a ƙungiyar ɗari-ɗari da ta dubu-dubu.
5
Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options