2 Sarakuna 8:7-15
7
Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,”
8
sai ya ce wa Hazayel, “Ɗauki wannan tare da kai ka tafi ka taryi mutumin Allah. Ka nemi nufin Ubangiji ta wurinsa; ka tambaye shi, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”
9
Sai Hazayel ya tafi taryen Elisha, ya ɗauka kyauta na kowane irin kaya masu kyau na Damaskus tare da shi a raƙuma arba’in. Ya shiga ya tsaya a gaban Elisha ya ce, “Ɗanka Ben-Hadad na Aram ya aike ni in tambaye ka, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”
10
Elisha ya amsa ya ce, “Je ka ce masa, ‘Ba shakka za ka warke’; ammaUbangiji ya nuna mini cewa ba shakka zai mutu.”
11
Sai ya zuba wa Hazayel ido har sai da Hazayel ya ji kunya. Sa’an nan mutumin Allah ya fara kuka.
12
Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”
13
Hazayel ya ce, “Yaya bawanka, wanda yake kare kawai, zai iya aikata wannan irin abu?” Elisha ya ce, “Ubangiji ya nuna mini cewa za ka zama sarkin Aram.”
14
Sai Hazayel ya rabu da Elisha ya koma wurin maigidansa. Da Ben-Hadad ya yi tambaya, “Me Elisha ya ce maka?” Sai Hazayel ya amsa, “Ya faɗa mini cewa tabbatacce za ka warke.”
15
Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.
Settings