2 Sarakuna 20:12-16
12
A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.
13
Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba.
14
Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”
15
Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.”
16
Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings