2 Sarakuna 18:23-25
23
“ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!
24
Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?
25
Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”
Settings