2 Korintiyawa 7:8-9
8
Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai.
9
Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.
Settings