2 Korintiyawa 7:13-14
13
Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.
14
Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya.
Settings