Skip to content
2 Tarihi 9:13-16

2 Tarihi 9:13-16

13
Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne,
14
ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon.
15
Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya.
16
Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options