2 Tarihi 31:5-8
5
Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa.
6
Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.
7
Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai.
8
Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila.
Settings