1 Sama’ila 9:6-10
6
Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.”
7
Shawulu ya ce wa bawan, “Idan muka isa can, me za mu ba wa mutumin? Ga shi abinci guzurinmu duk ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu kai wa mutumin Allahn nan. Me muke da shi?”
8
Bawan ya sāke ce masa, “Duba ina da kwatar azurfar da zan ba wa mutumin Allah don yă gaya mana wace hanya ce za mu bi.”
9
(A dā a Isra’ila, in wani yana so yă nemi nufin Allah, mutumin yakan ce, “Zo mu tafi wajen mai duba.” Gama wanda ake ce da shi annabi a yanzu, a dā ana kiransa mai duba ne.)
10
Shawulu ya ce wa bawansa, “Madalla, zo mu tafi.” Sai suka kama hanya suka nufi birnin da mutumin Allah yake.
Settings