Skip to content
1 Sama’ila 12:6-12

1 Sama’ila 12:6-12

6
Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutane, Ubangiji ne ya naɗa Musa da Haruna suka fitar da kakanninku daga Masar.
7
Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku.
8
Bayan da Yaƙub da ’ya’yansa suka shiga Masar suka yi kukan neman taimako daga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya aika musu da Musa da Haruna. Su ne suka kawo kakanni-kakanninku daga Masar suka zauna a nan.
9
Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su.
10
Suka yi kuka a gaban Ubangiji suka ce, “Mun yi zunubi mun bar Ubangiji, muka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Amma ka cece mu yanzu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
11
Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya.
12
Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options