1 Sama’ila 10:2-7
2
Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’
3
“Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
4
Za su gaishe ka, su ba ka burodi biyu, kai kuwa sai ka karɓa.
5
“Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci.
6
Ruhun Ubangiji zai sauko a kanka da iko, za ka kuma yi annabci tare da su. Za a canja ka ka zama dabam.
7
Da zarar waɗannan alamu sun cika, sai ka aikata duk abin da kana iya yi gama Allah yana tare da kai.
Settings