1 Sarakuna 8:22-40
22
Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama,
23
ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.
24
Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau.
25
“Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’
26
Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina tă cika.
27
“Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina!
28
Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana.
29
Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri.
30
Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.
31
“Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan,
32
sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa.
33
“Sa’ad da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila a yaƙi saboda sun yi maka zunubi, sa’ad da kuma suka dawo gare ka don su furta sunanka, suna addu’a suna roƙo gare ka a wannan haikali,
34
ka ji daga sama, ka gafarta zunubin mutanenka, ka kuma dawo da su ƙasar da ka ba wa kakanninsu.
35
“Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su,
36
ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.
37
“Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo,
38
in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali,
39
sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi wani abu. Ka yi da kowane mutum bisa ga dukan abin da ya yi, tun da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan dukan mutane),
40
saboda su ji tsoronka a kowane lokacin da suke zaune a ƙasar da ka ba wa kakanninmu.
Settings