Skip to content
1 Sarakuna 18:7-16

1 Sarakuna 18:7-16

7
Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?”
8
Iliya ya amsa, ya ce, “I, je ka faɗa wa maigidanka cewa, ‘Iliya yana a nan.’ ”
9
Obadiya ya yi tambaya, “Me na yi da ba daidai ba, da kake miƙa bawanka ga Ahab don yă kashe?
10
Na rantse da Ubangiji Allahnka, babu al’umma ko masarauta da mai girma sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka can, sai yă sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.
11
Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’
12
Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi.
13
Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa.
14
Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!”
15
Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.”
16
Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options