1 Sarakuna 16:17-20
17
Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto.
18
Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.
19
Wannan ya faru saboda zunuban da ya yi, ya yi mugunta a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubin da Yerobowam ya yi da ya sa Isra’ila suka yi.
20
Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Settings