1 Sarakuna 14:1-5
1
A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo,
2
sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane.
3
Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4
Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa.
5
Amma Ubangiji ya ce wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa tă tambaye ka game da ɗanta, gama yana ciwo, za ka kuwa ba ta amsa kaza da kaza. Sa’ad da ta iso za tă yi kamar wata ce dabam.”
Settings