1 Yohanna 1:5-10
5
Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.
6
In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.
7
Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
8
In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.
9
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
10
In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
Settings