1
To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.
2
Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba.
3
Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.