1 Tarihi 4:1-6
1
Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.
2
Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa.
3
Waɗannan su ne ’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash. ’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni.
4
Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.
5
Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.
6
Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.
Settings