1 Tarihi 29:22-25
22
Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.
23
Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya.
24
Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.
25
Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.
Settings