1 Tarihi 29:10-20
10
Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin.
11
Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12
Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
13
Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
14
“Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
15
Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.
16
Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.
17
Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.
18
Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.
19
Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
20
Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki.
Settings