Skip to content
1 Tarihi 26:1-8

1 Tarihi 26:1-8

1
Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza.
2
Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
3
Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.
4
Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,
5
Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)
6
Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
7
’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.
8
Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options