Skip to content
1 Tarihi 26:1-10

1 Tarihi 26:1-10

1
Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza.
2
Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
3
Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.
4
Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,
5
Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)
6
Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
7
’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.
8
Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
9
Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.
10
Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options