Skip to content
1 Tarihi 24:1-6

1 Tarihi 24:1-6

1
Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
2
Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
3
Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
4
Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
5
Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
6
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options