1 Tarihi 24:1-13
1
Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
2
Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
3
Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
4
Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
5
Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
6
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
7
Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,
8
na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,
9
na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,
10
na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,
11
na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,
12
na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,
13
na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
Settings