1 Tarihi 14:13-17
13
Filistiyawa suka sāke kai hari wa kwarin;
14
sai Dawuda ya sāke roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa, “Kada ka tafi kai tsaye, amma ka yi zobe kewaye da su, ka kuma fāɗa musu a gaban itatuwan tsamiya.
15
Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.”
16
Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer.
17
Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa.
Settings