1 Tarihi 14:11-12
11
Saboda haka Dawuda da mutanensa suka haura zuwa Ba’al-Ferazim, a can kuwa suka ci Filistiyawa da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa kan raraki ƙasa, haka Allah ya raraki abokan gābana ta wurin hannuna.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
12
Filistiyawa suka yashe allolinsu, Dawuda kuma ya ba da umarnai a ƙone su a wuta.
Settings