1 Tarihi 1:8-16
8
’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.
9
’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan
10
Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.
11
Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa,
12
Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.
13
Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa,
14
Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa
15
Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
16
Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.
Settings