Tsallake zuwa abun ciki

Zabura96

Kira ga dukan duniya su yabi Allah su kuma yi shelar bishara

1
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2
Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

Matsayin Yahweh mafi girma bisa gumaka

4
Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
5
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

Ku yi sujada ku kuma furta ɗaukakar Allah

7
Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.
8
Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.
9
Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.

Ubangiji yana mulki yana zuwa ya yi hukunci

10
Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.
11
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
12
bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
13
za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options