Zabura 96
Kira ga dukan duniya su yabi Allah su kuma yi shelar bishara 1–3
1
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2
Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
Matsayin Ubangiji mafi girma bisa gumaka 4–6
4
Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
5
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
Ku yi sujada ku kuma furta ɗaukakar Allah 7–9
7
Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.
8
Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.
9
Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.
Ubangiji yana mulki yana zuwa ya yi hukunci 10–13
10
Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.
11
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
12
bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
13
za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Study note