Skip to content

Zabura150

Inda da Dalilin Yabon Allah

1
Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2
Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

Kayan Aikin Yabo

3
Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,
4
yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5
yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

Yabon Allah na Dukan Halitta

6
Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options