Zabura 89:19-37
19
Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane.
20
Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi.
21
Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi.
22
Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi.
23
Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa.
24
Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi, kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa.
25
Zan sa hannunsa a bisa teku, hannunsa na dama a bisa koguna.
26
Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’
27
Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.
28
Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.
29
Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan.
30
“In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,
31
in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,
32
zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala;
33
amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.
34
Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata.
35
Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,
36
cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;
37
zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” Sela
Settings