Skip to content
Zabura 65:6-13

Zabura 65:6-13

6
wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,
7
wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.
8
Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.
9
Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.
10
Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.
11
Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.
12
Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna.
13
Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options