Zabura 58:1-2
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?
2
Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.