Skip to content
Zabura 55:1-8

Zabura 55:1-8

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;
2
ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis
3
hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.
4
Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.
5
Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.
6
Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,
7
da na tafi can da nisa na zauna a hamada; Sela
8
da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options