Zabura 48:1-7
1
Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
2
Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki.
3
Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
4
Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,
5
sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
6
Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
7
Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
Settings