Zabura 18:37-42
37
Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su.
38
Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna.
39
Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini.
40
Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana.
41
Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.
42
Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna.
Settings