Skip to content
Zabura 18:29-45

Zabura 18:29-45

29
Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga.
30
Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
31
Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?
32
Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.
33
Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli.
34
Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
35
Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
36
Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya.
37
Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su.
38
Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna.
39
Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini.
40
Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana.
41
Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.
42
Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna.
43
Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina,
44
da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana.
45
Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options