Skip to content
Nehemiya 7:66-72

Nehemiya 7:66-72

66
Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,
67
ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245.
68
Akwai dawakai 736, alfadarai 245
69
raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720.
70
Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci.
71
Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki.
72
Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options