Skip to content
Markus 14:26-31

Markus 14:26-31

26
Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
27
Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’
28
Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
29
Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
30
Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyukai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”
31
Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options