Skip to content
Luka 24:1-8

Luka 24:1-8

1
Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.
2
Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.
3
Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.
4
Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.
5
A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?
6
Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,
7
‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ”
8
Sai suka tuna da maganarsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options