Skip to content
Luka 19:29-31

Luka 19:29-31

29
Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu,
30
“Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan.
31
In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options