Skip to content
Luka 13:34-35

Luka 13:34-35

34
“Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
35
Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.