Firistoci 8:6
Ana nuna aya 6 tare da mahallin da ke kewaye.
3
ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.”
4
Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada.
5
Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6
Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da ’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa.
7
Ya sa wa Haruna taguwa, ya ɗaura igiya kewaye da shi, ya sa masa riga, ya sa masa efod. Ya kuma ɗaura masa efod wanda aka yi masa saƙar gwaninta.
8
Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin.
9
Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
Settings