Skip to content
Firistoci 8:1-13

Firistoci 8:1-13

1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti,
3
ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.”
4
Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada.
5
Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6
Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da ’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa.
7
Ya sa wa Haruna taguwa, ya ɗaura igiya kewaye da shi, ya sa masa riga, ya sa masa efod. Ya kuma ɗaura masa efod wanda aka yi masa saƙar gwaninta.
8
Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin.
9
Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
10
Sa’an nan Musa ya ɗauki man keɓewa ya keɓe tabanakul da kuma kowane abin da yake cikinsa, ta haka ya tsarkake su.
11
Ya yayyafa mai a kan bagade sau bakwai, yana keɓe bagade da dukan kayayyaki, da daro, da abin da yake tsaya a kai, don yă tsarkake su.
12
Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya kuma keɓe shi don yă tsarkake shi.
13
Sa’an nan ya kawo ’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options