Skip to content
Firistoci 26:40-45

Firistoci 26:40-45

40
“ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,
41
waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,
42
zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.
43
Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina.
44
Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu.
45
Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options