Skip to content
Firistoci 26:3-13

Firistoci 26:3-13

3
“ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina,
4
zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.
5
Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.
6
“ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba.
7
Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku.
8
Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku.
9
“ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku.
10
Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo.
11
Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba.
12
Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena.
13
Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options